Powered By Blogger

abdul

Abdul

Search This Blog

Pages

Popular Posts

Translate

Wednesday, 9 October 2013

MATSAYIN TAUHIDI
assalamun alaikum yan uwana ,bayan gaisuwa irin ta addinin islam ,iname farawa da sunan allah merahama da jinqai ,tsira da amunci su qara tabbata ga fiyayyan halitta annabi muhammadu s.a.w tare da sahabban sa da wadanda sukai ruqo da hanyar su .har izuwa qarshen duniya
yan uwa wannan wani abune (tauhidi)wanda dayawan mutane suke tambaya ko mamaki akan yadda malamanmu na sunnah suketa bayani ba dare ba rana akan tauhidi kuma ba sa sassauci ga dukwanda yasabawa tauhidi na haqiqa suka qare rayuwar su akan lallai akiyaye akuma kula da tauhidi akansane wasu malaman suka mutu akurkuku kamar su sheikul islam ibn taiymiya ,wasu sunbar mahaifarsu kamar su muhammad dan abdulwahab. Wasu andake su an dauresu ,kamar su imam tirmidi ,ahamad dan hambali ,ga irin su sheik jafar mahamud adam, r.h sheik mahamud gumi r.h hakama can qololuwa sama (sahabban manzon allah s.a.w)kamar su salmanur farisi ,abuzarri giffari ,sumaiya ,bilal .dadai shauran su allah ya qara yadda dasu .yan uwa wadannan dukkansu sunsha fama meyawa akan tabbatar da tauhidi. Dayawa yan uwa musulmi sunyi bacci akan tauhidi harma wasu suke ganin malamanmu nasunnah suna zafafawa kamar su sheik,ibn taiymiyya ,muhammad dan abdulwahab ,usaimin,bin bath,saleh al usaimi, fauzanul alfauzan,nasiridden albani da su sheik jafar adam,dr ahamad b.u,k, sheik isa aliyu fantami ,binu usman,albani zaria,dr jalo jalingo,saleh pakistan,sheik gero arugungu,sheik harun kabiru kombe da dai shauransu,.
Yan uwa musani tauhidi shine turakun addini musulunci kuma shine shisshiken musulunci in ba tauhidi to ba musulunci,hakama koda ka shekara kana sallah, ko azumi, laiya,zikiri,karatun qur'ani , koda kana ciyar da mutane da halal adadin wadanda sukaje maka hajji, .in ba tauhidi to mutum yayi abanza dan allah bazai karba ba hasalima azaba za aiwa mutum ,sannan babu abu mafi sauqin warwarewa kamar tauhidi, azumi yana karyewa da cin abunci ,kusantar iyali dashauran su ,sallama na karyewa da hadasi amma tauhidi na iya karyewa qasa da second din agogo ,wannan dalilinne yasa allah swt yaita ja mana kunne a alqurani me girma kamar a suratul
.1 ,anbiya'i aya ta 25 data 66
. 2.huda ayata 25 zuwa ta 26
.3. Zariyat aya ta.56
. 4.sa'ad aya ta 17
.5. Nahali ayata 36
.6.al'israa ayata 23
.7.nisa'i 36
.8. Albaqara ayata 256
9. Al an'am ayata 151 data 153
.10. Yunusu ayata 106
.11 zumar ayata 3.
12. Annahali ayata 120
13. Annisa'i ayata 116
14.yusuf ayata 108
15.al israa aya ta 57
16 al an'am 162 da 163
.yan uwa akwai ayoyi dadama da hadisai ingantatu da suke nuna matsayin tauhidi da yadda allah s.w.t yai ta tsoratar damu akan tauhidii yaita nanata mana muriqe tauhidi .dan hakane ma allah s.w.t ya turo dukkanin annabawa da manzannin sa,akan tauhidine annabawa da manzanni suka shawuya , wasu akakashesu wasu sukai hijira suka bar mahaifarsu akanhakane wasunsu suka bata da iyayensu da yayan su.
ashe kenan yan uwa kunga tauhidi ba abune wanda za ai wasa dashi ba hakan tasa dolene malamanmu nasunna suka dage akan yadashi dankoyi da annabawa da manzanni .
Abubuwan da zamu kula dasu dan kiyaye tauhidimmu
.1.dole mu guji shirka babba daqaramar ta
2.mukiyaye bidiah dan itace silar shirka
3.mu yawaita neman ilmi da bayani akan tauhidi agun malamai
allah ka qara tsira da amunci ga fiyayyan halitta annabi saw.kasamu cikin ceton sa s.a.w kakuma karemana malamanmu na sunnah
wslm.

.

No comments:

Post a Comment